Aci gaba da fafata wasannin share fage da akeyi a sassa daban-daban na ƙasar nan kuma na gwamnoni daban-daban a kusancin ƙasar nan da arwacin ƙasar nan.
A jiya dai an fafata wasa mai zafi tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Plateau United da Niger Tornadoes. Sai dai awasan Niger Tornadoes ta ragargaza ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Plateau United daci 1 mai ban haushi.
Bayan tashi daga wannan wasa jaridar www.koginwasanni.com.ng ta tattauna da mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Niger Tornadoes wato Abubakar Bala ina ya bayyanamana cewa:
“Naji daɗin nasarar da ƙungiyata ta Niger Tornadoes ta samu akan Plateau United a wannan wasa na share fage. Kuma wannan wasa tabbas zai taimakamana ta yadda idan munfara fafata gasar NNL da kuma gasar ajin Firimiya ta ƙasa wato NPFL duba da yadda kowacce ƙungiya kamar taci babu ganin yadda kowacce ta kwashe lokaci mai tsayi batare da ta buga wasa na”
Awasan farko dai Niger Tornadoes tayi rashin nasara inda awasa na biyu kuma tayi nasara. A gobe Talata zata fafata wasa na uku kuma tana buƙatar nasara domin fitowa daga rukuninsu.