Kungiyar Barcelona sun tabbatar da cewa Lionel Messi ya yi rauni, kuma ba zai samu buga wasansu na karshe ba na shekarar 2020 da za su buga da Eibar.
Sai dai ana sa ran zai buga wasan Barcelona farko a 2021 wanda za su buga da Huesca a ranar 3 ga watan Janairu.
Barcelona ta bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta a ranar Lahadi, inda ta tabbatar da cewa Messi ba zai buga wasan kungiyar da Eibar ba.
Wasan Barcelona da Eibar din zai zo ne a ranar 29 ga watan Disamba.