Dan wasan kasar Portugal, kuma mai buga Tamola a kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar dan wasan karni bayan da ya doke Lionel Messi a taron bada kyautar ta 2020 ta ‘Globe Soccer Awards’.
Sauran ‘yan wasan da Ronaldo ya doke sun hada da Ronaldinho na Brazil, da kuma Mohamed Salah da Misra da Liverpool.
Taron ya gudana ne a Dubai. Inda aka bayyana Ronaldo a matsayin wanda ya rika lashe dan wasa mafi kwazo tun daga shekarar 2001 har zuwa 2020. Ya kuma lashe gasar zakarun Turai sau 5 a Man United da Real Madrid, da kuma Firimiyar Ingila sau uku a Manchester United, da kuma La Liga guda biyu a Real Madrid, da kuma kofin Nations League da ya lashe da kasarsa Portugal.
Ronaldo ya mika godiyarsa ga kowa da kowa da kuma iyalinsa da mahaifiyarsa da ‘yar’uwarsa. Ya ce; wannan kyautar da aka ba shi babbar kyauta ce. Ya ce a karramaka a ce kai ka fi kowa, lallai babban al’amari ne.