Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ce za ta fara yi wa sabbin membobinta rijista a ranar 25 ga watan Janairu domin ganin ta tattara ‘ya’yan jam’iyyar waje guda domin kasance tsintsiya madaurinki daya domin fuskantar zaben 2023.
Jam’iyyar ta APC ta bayyana hakan ne a cikin sakon sabuwar shekara da ta fitar ta hannun Sanata John Akpanudoedehe, Sakataren kwamitin tsare-tsare da shirya taro, CECPC a ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce tuni suka fara sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar inda suke son hada kawukansu domin kasance jam’iyyar mai karfin fada a ji a shirye-shiryen zaben 2023.