Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa bisa rasuwar Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu da kuma Talban Zazzau, Abubakar Pate.
Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban kasar, shi ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja, inda ya bayyana rasuwar a matsayin abin bakin ciki mai firgitarwa da ya auku.
Ya ce; “rasuwar fitattun mutane biyu a masarautar Zazzau jim kadan da rasuwar Sarki Shehu Idris ya firgita ni matuka. Ina mika sakon alhini da ta’aziyyah ga iyalan wadannan shugabanni biyu, da kuma masarautar Zazzau da gwamnatin jihar Kaduna da al’ummar jihar”. Ya bayyana.
Inda shugaba Buhari ya yi musu addu’ar Allah ya jikansu da Rahama yasa aljanna makoma ne. Malam Garba Shehu ya ce; shugaba Buhari zai aikata da tawaga a madadinsa domin zuwa mika sakon ta’aziyyah.