Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa matsalar tsaro ya taimaka sosai wajen kassarar tattalin arzikin kasarnan. Inda ya ce matsalar na hana masu zuba hannun jari su zuba jarinsu.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a sakon sabuwar shekara da ya aikewa al’ummar Nijeriya, inda ya ce ko shakka babu shekarar da ta gabata ta 2020 na cikin jerin shekarun da al’umma suka sha matukar wahala, kama daga matsalar tsaro da matsin rayuwa baya ga karancin walwala.