Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe a ranar Lahadi sun ce sun yi nasarar cafke mutum 318 bisa zarginsu da aikata laifuka mabambanta a cikin shekarar 2020.
Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar yana mai bayyana nasarorin da ‘yan sandan suka samu a cikin shekarar 2020.
Ya kara da cewa daga cikin laifukan da ake zargin wadanda suka kama sun hada da kisan kai, fyade, garkuwa da jama’a, sata, fashi da makami, da kuma rikicin Fulani da makiyaya.
Ya tabbatar da cewa sun yi nasarar gabatar da mutum 250 a gaban kuliya, a yayin da 187 ake ci gaba da shari’arsu.
Abdulkarim ya ce mutum 68 kuma ana nan ana ci gaba da bincikensu a yayin da kuma 63 tuni aka yanke musu hukunci suna ci gaba da zaman jarun. Ya kuma tabbatar da cewa mutum 39 kuma an maida bincikensu ofishin Daraktan shigar da kararraki da shawarwari na jihar.