An horas da Malaman firamare dubu uku da dari biyar da hamsin da biyu a jihar Oyo a wani mataki na shirye-shiryen komawa makaranta.
Taron horaswar an kwashe mako daya ana yi domin bunkasa ilimin firamare a jihar..
Dr Nureni Adeniran, shugaban hukumar SUBEB na jihar, a ranar Litinin a garin Ibadan, ya ce horaswar ya gudana ne a karkashin hukumar tare da hadin guiwar UBEC.
Ya ce sun kuma shirya taron horaswar karkashin shirin SUBEB na bunkasa koyarwar a jihar. Adeniran ya ce horaswar ya fara gudana ne a ranar 4 ga watan Janairu domin fuskantar sabon zangon karatun da za a shiga wajen bunkasa ilimi a jihar.