A ranar Talata gwamnatin Borno ta bada tallafin kayayyaki da kudi ga iyalai goma sha daya da ‘yan Boko Haram suka kashe su.
‘yan ta’addan Boko Haram a ranar Asabar sun kari hari a kauyen Pemi dake karamar hukumar Chibok, inda suka tarwatsa gine-gine da kuma sace wani Malami da wata diya.
Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Usman Kadafur, shi ne ya gabatar da tallafin, inda ya jajantawa iyalan tare da bayyana harin da aka kai musu a matsayin abin bakin ciki.
Kadafur wanda ya samu rakiyar Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a jam’iyyar APC, ya bada tallafin mota kirar Hilux ga ‘yan sa kai a kauyen, da kuma miliyan 1.1 ga duk iyalai goma sha daya da Boko Haram ta kashe.