Rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun cafke mutum 12 bisa zarginsu da fashi da makami a yayin da kuma suka kama mutum bakwai bisa zarginsu da wadansu laifukan.
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna, shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano, inda ya ce wadanda ake zargi, masu atisayen Puff Adder daga jami’an ‘yan sandan ne suka kama su.
Haruna ya ce mutum 12 da ake zargi da fashi da makami an kama su ne a Sharada da Sabon gari da kuma Sauna duk a cikin garin Kano. Ya ce sun kware wajen fashin wayoyi da addabar mutane.
Ya ce wadanda ake zargi an kama su da muggan makamai.
Har wala yau ‘yan sandan sun gabatar da masu siyar da kwayoyi ga wadanda ake zargi da fashin.
Sannan Kakakin ‘yan sandan ya ce sun kama wani mai shekaru 19 da ya damfari wani dan kasuwa mai suna Auwalu Abdulmalik da Buhari Yusuf naira dubu dari uku da talatin.