Cibiyar dake dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC ta bayyana cewa a awa 24 an kara samun mutum 1,634 da suke kamuwa da cutar korona, lamarin da ya sanya ya zuwa yanzu wadanda suka kamu da cutar a kasar tun bayan bullarta sun kai 133,552.
NCDC sun tabbatar da hakan ne a shafinsu na Twitter a daren ranar Talata.
NCDC sun ce ya zuwa yanzu an yi wa mutum miliyan daya da dubu dari uku da biyu da dari hudu da goma gwajin cutar tun bayan tabbatar da bullar cutar a ranar 27 ga watan Fabarairun 2020.
Mutum 1,634 da aka samu da cutar cikin awa ashirin da hudu sun fito ne daga jihohi 25 ciki harda birnin tarayya Abuja.
Legas ke da kaso mafi yawa da mutum 440, sai Anambra da FCT, 158 da Rivers, 134.
Sauran sun hada da Abia-103, Oyo-90, Enugu-81, Osun-73, Gombe-54, Kwara-50, Ogun-32, Plateau-32, Akwa Ibom-31, Ondo-24, Borno-23, Delta-23, Ebonyi-21, Taraba-21, Bayelsa-16, Kaduna-15, Nasarawa-13, Jigawa-12, Bauchi-11, Kano-11, Zamfara-4 da Sokoto-2.