Ana Ci gaba da samun Ruɗani a Jihar Kwara yayin da Kiristoci suka bijire wa umarnin gwamnati na sake bude makarantu bayan rufe su na wani lokaci.
A halin da ake ciki Malamai Kiristoci da suka yi fitar farin dango don zanga-zanga bisa matakin da gwamnatin ta dauka na sake buɗe makarantun sun hana dalibai da Malaman su shiga makarantu a yau Laraba.
Malamai Kiristocin da suka fito zanga-zangar dai suna ɗauke ne da Kwalaye dake nuna rashin amincewar su da umarnin gwamnatin Jihar na sake buɗe makarantun.
Kuma Wannan matakin Zanga-zangar Kiristocin ya haifar da hatsaniya a wata makaranta mai suna “Baptist School” dake Surulere to sai dai daga bisani yan sanda sun yayyafa wa al’amarin ruwa.
Kawo yanzu dai gwamnatin Jihar ta Kwara ba ta ce uffan ba dangane da wannan al’amari, to sai dai umarnin nata ya zo a daren jiya Talata ta hannun ma’aikatar ilmin Jihar.
Sanarwar ta ce gwamnati ta ɗauki matakin rufe makarantun ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma sakamakon rudani da haramta sanya Hijabi da wasu Makarantu suka kawo.
Gwamnatin ta Kara da cewa Kowace daliba Musulma tana da yancin saka Hijabi ta shiga Makaranta wanda kuma hakan shine zaman lafiya zai wanzu.