Kwamitin Koli dake kula da harkokin addinin Musulunci na Kasa ya ce ba za ta tilasta wa kowa karbar rigafin Corona ba.
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Alhaji Sa’ad Abubakarwanda shine shugaban kwamitin shi ya bayyana matsayar kwamitin yayin wani taro da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.
Kuma yana wannan m,agana ne a gaban Sakataren Gwamnatin Kasar nan Boss Mustapha, Ministan Lafiya Dakta Osagie Ehanire da kuma babban Darakatn hukumar kula da lafiya matakin farko ta tarayya Dakta Faisal Shu’aib.
A cewar Alhaji Sa’ad Abubakar Kwamitin Kolin Kula da harkokin Addinin Musulunci ya yi amanna da allurar rigafin to amma fah ya ce bai isa tursasa wa kowa yin sa ba.
Wannan taro da ya gudana dai ya zo ana tska da tirk-tirkar alfanu da kuma illar rigafin, dalilin hukumomin kasar kenann na tsara wannan zama manyan Limamai da Shehunan addinin Musulunci don neman goyon bayan su.
Da yake tofa albarkancin bakin shi yayin Zama Sakataren Gwamnatin Taryayya Boss Mustapha wanda shine shugaban Kwamitin yaki da cutar Corona na Fadar Shugaban Kasa, ya ce a yanzu haka an gama duk abinda ya dace na fara yiwa Malaman addinini da sarakunan gargajiya wannan allura.
Ya kara da cewa za a yi hakan ne don ganin an karfafa gwiwa wa sauran mabiya kan karbar rigafin.