Rundunar Yan Snadar Jihar Benuwe ta sanya dokar hana Achaba a birnin Makodi fadar gwamnatin jihar daga karfe karfe takwas na dare zuwa shida na safe.
Wannan doka ta biyo bayan ci gaba da samun ayyukan bata gari wanda ake alaknta shi da yadda ake amfani da babur.
Cikin wata sanarwa dake daquke da sanya hannun mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Catherine Anene ta ce la’akari da yawaitar ayyukan bata gari ne daga karfe takwas zuwa wayewar gari ya sa aka dauki wannan, inda kuma ta umarci duk wadda ya karye dokar to ya kwana da sanin cewa sai ya dandana kudar shi.
Sanarwar ta ce a shekara ta 2016 ne dai Gwamnan Jihar Benuwe a wanchan lokacin ya kafa dokar hana zirga ziregar yan achaba daga karfe takwas zuwa shida na safe a birnin na Makodi.
“Mun dauki wannan mataki ne lura da yadda miyagun ayyuka ke kara yawaita a fadar jihar Benuwe wadda kuma ana amfani da babur ne wajen aikata su, ciki har da kisan gilla da aka yi wa Babban Mai Baiwa Gwamna Shawara kan harkar tsaro Dr. Denen Igbana, wanda makasan sun zo ne su ma a kan babur” Inji sanarwar.
Ta kara da cewa “Mu a matsayin mu na runduna, dole ne mu tada jama’a su farka daga barcin da suke domin wannan doka tana nan daram babu abinda ya same ta, kuma duk wanda ya saba toh zai gane kuren sa.”
Idan za a iya tunawa dai shi ma Gwamnan jihar na yanzu Samuel Ortom ya sanya dokar haramta achaba da kuma ayyukan yan Tasi da aka fi sani da Duck-Nyash a kananan hukumomin Sankera, Katsina-Ala, Ukum da kuma Logo biyo bayan kisan gillar da aka yi wa dan uwan Sanata Gabriel Suswan a wadannan yankuna.