A daren jiya jumm’a ne sarkin kano Muhammadu Sunusi ya taya gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje murnar lashe zaben gwamnan jihar kano da yayi karo na biyu.
Shuwagabannin biyu sun taya junan su murnar kammala azumin watan ramadan da bikin karamar sallah da al’ummar musulmi ke gudanarwa.
Sannan shuwagabannin sunyi kira ga daukacin al’ummar musulmai da suyi koyi da darussan da suka samu a watan ramadan mai albarka.
Daga karshe sarkin kano Muhammadu Sunusi yayi wa gwamnan fatan samun nasara a wa’adin mulkinsa karo na biyu.
Idan ba a manta ba shuwagabannin biyu basa ga maciji da juna tun lokacinda gwamnan yayi zargin sarkin na goyon bayan ‘dan takarar gwamnan jihar kano a karkashin jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf. Hakan ya janyo rarrabuwar masarautar jihar kano gida biyar wanda ya ragewa sarki Sunusi karfin iko.
Daga baya kuma aka bullo da wasu tuhume tuhume akan sarkin wanda hakan yaso yayi awon gaba da rawanin sarkin inda saida shugaba Buhari da wasu manyan kasar nan suka sa baki domin sulhunta manyan jagororin biyu.