Gwamnatin tarayya ta yi wa manoma a ƙalla sama da Miliyan bakwai da aniyar sanya su cikin tsarin tallafin noma na gwamnatin.
Wannan Jawabi ne yana zuwa ne ta bakin Ministan Noma da Bunƙasa harkokin Karkara Sabo Nanono yayin wani taron dukkanin manoma wanda Ƙungiyar Manoma ta Kasa AFAN a takaice ta shirua yau Juma’a a Birnin Kanon Dabo.
A cewar Ministan, gwamnati ta ɗauki mataki yiwa manoman rajistar ne don ganin ta janyo su a jiki da zummar basu damar sharbar romon tallafin noma na gwamnatin tarayya.
Nanono ya yaba wa Ƙungiyar AFAN bisa wannan Ƙoƙari nata wajen shirya taron, inda ya bukaci jagorancin Ƙungiyar ta kasa da kada ya nuna fifiko a yayin mulkin sa.
Daga nan Nanono sai ya bukaci dukkannin Manoma a kasar nan da su haɗa karfi da karfe don daukaka kasar izuwa munzali mai nagarta a harkar noma.
A bangaren sa Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje wanda Mataimakin Sa Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya alkawarta cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bada gudunmawar ta wa manoma, don ganin an samun ci gaba a farnin noma.
Ganduje ya ce a yanzu haka gwamnatin sa ta ɓullo da wasu tsare tsaren kimiyya da kuma karin ilmi da za su taimaka wajen ragen asaar amfanin gona da ake samu