Daga Sulaiman Musa
Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta bayyana cewa babu wata gwamnati da ta shimfida shugabanci na kwarai a Nijeriya kamar gwamnatin Muhammadu Buhari.
Sannan, APC ta kuma zargi jam’iyyun adawa da kokarin kawo sanya siyasa cikin lamarin samun nasarar shugaba Buhari.
Shugaban APC na rikon kwarya, Gwamna Mai Bala Buni shine ya shaida hakan a ranar Talata yayin wani taron ganawa na jam’iyyar.
Buni, ya bayyana cewar babu wani da zai gamsu cewa akwai wata gwamnatin da ta fi ta Buhari kokarin kyautata Nijeriya.
Buni wanda ya samu wakilcin sakataren riko na jam’iyyar, Sanata John James Akpanudoedehe, ya bayyana cewar jam’iyyarsu ta zo da tsare-tsaren da suka dace na kyautata rayuwar al’umman Nijeriya a karkashin jagorancin Buhari.