Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya ce tabbas Najeriya ta yi rashin haziki, nagartacce kuma shugaba na kwarai.
Alhaji Atiku Abubakar na wannan kalamai ne daidai lokacin da yan Najeriya ke ci gaba da alhinin cika shekaru goma sha daya da rasuwar Tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umar Musa Yar’adua.
Ya ce tabbas babu ko shakka yan Najeriya za su ci gaba da tuna marigayi Yar’adua bisa irin jajircewar shi da kuma tsayuwar daka wajen gina al’umma tare da kyawawan halayensa.
Cikin Wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Atiku ya danganta Yar’adua a matsayin mai kishin kasa tare da fatan Allah Ya rahamshe sa.
Sakon shi “Yau shekaru goma sha daya da rasuwar tsohon shugaban kasar mu, marigayi Umaru Musa Yar’adua. Shugaba Mai kishin kasa da tausayi.
Za mu ci gaba da tuna ka, domin waiwaye kan halayen ka”
“Allah ya jikansa, ya gafarta masa. Ameen”
Alhaji Umar Musa Yar’adua dai ya dare karagar mulkin Najeriya ne a shekara ta 2007 inda ya shafe shekara biyu da rabi yana mulkar kasar.
To amma babu lungu da sako da mutum zai shiga ba tare da jin ana mishi fatan alkhairi bisa jajircewar sa a dan wanchan lokacin ba.