WASU MAYAKA DAKE DELTA SUN GARGADI FULANI, SANNAN SUNYI ALKAWARIN BADA KARIYA GA ‘YAN JAHAR it
Wata kungiyar mayaka ta MEDND dake jihar Delta tasha alwashin ramawa duk wanda ‘yan ta’adda suka kashe ko aka rusawa gida a jahar.
Shugabann kungiyar gwamnonin Inyamurai SMBLF watau Chief Edwin Clark ya bayyana cewar bazasu yarda da masu kiwo shiga yankin ba.
Wannan ya biyo bayan dokar da ‘yan kungiyar UYLA ta saka cewar duk wani fulani dasu tattara shanunsu su bar yankin nan da awa 48.
KARANTA WANNAN:-
An kama matashi na sata a ranar farko da ya fara zuwa bayan an daukeshi aiki
Shugaban rundunar ‘yan sanda ta jihar Delta Muhammad Aliyu yayi alwashin kawo zaman lafiya a jihar baki daya.
Labari yazo Kan harinda makiwatan suka Kai a wasu kauyuka na Asaba da Agbor dake jihar Deltan, hakan ya biyo bayan nuna amincewa da gwamna jihar yayi ne na dokar hana kiwo a yanki.
Sannan makiyayan sun sha alwashin cigaba da Kai hare-haren matukar gwamnan bai janye dokar tasa ba nan da tsawon awa 72.
Gwamnan yace idan abunda kuka fada dagaske ne yazama wajibi mu kori duk wani makiyayi a yanki, yakara da cewa idan kuka kashe mutum daya to sai mun kashe goma idan Kuma kuka kona gida daya sai mun Kona naku goma. Duk idan kukai abu daya sai mun nunkashi sau goma.
Bazamuyi wasa da alkwarin da muka dauka ba zamu iya wargazaku a kowane lokaci. Domin kishin NIGER DELTA, Kuma zamuyi duk abunda zamu iya don baiwa jihar kariya.
KU KARANTA WANNAN:-
Dubu Sittin aka bamu mu kashe wani mutum: in ji wasu mutane a Kebbi
Jami’an rundunar tsaro ta Civil Defense a Jihar Kebbi sun yi nasarar chafke mutane biyu da aka yi hayarsu su lashe wani mutum.
Mutane dai an yi kwangilar su da aniyar hallaka wani mutum mai suna Gari Mamman mazaunin kauyen Lahore dake karamar hukumar Zuru ta Jihar ta Kebbi.
Kwamandan rundunar ta Civil Defense Alhaji Suleiman Ibrahim Marafa ya ce bisa bayanai da suka samu a gurin wadanda ake zargin, wani mutum ne mai suna Alhaji Mamman ya yi hayarsu da zummar wancan aika-aika, inda ya basu fashin alkalami naira dubu sittin cikin dubu tamanin da aka yi yarjejeniya.
Ya ce mutanen biyu masu suna Mando da Manu, sun banka wa gidan Gari Mamman amma daga bisani sun fahimci cewa ba ya gida.
Sai dai a wata tattaunawa da manema labarai, wanda ya bada kwangilar kisar ya musanta zargin, inda ya ce shi dai tura su ya yi su koya mishi hankali ba wai kashe shi ba.
Ya ce kuma dalilin shi na haka shine, yana zarginsa ne da hallaka mishi mahaifi watanni uku da suka wuce.