Daga Uzairu Dauda Bunga
Asusun tallafawa ilimin yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ta bakin shugaban tawagar wayar da kan matasa karkashin Asusun jahar Kano, Ni’imatullah Bala Umar, ya yaba da irin tsarin matakan da Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje kebi don inganta fannin ilimi.
Tawagar ta matasan, da Asusun UNICEF ya kafa tare da daukar nauyi, ta hanyar kwararrun mata masu ilimi HILWA da hadin gwiwar hukumar kula da ilimin bai daya ta jahar Kano SUBEB na burin karfafawa tsarin makarantu da shirye shiryen da zasu inganta ilimi daga tushe acikin al’umma.
Bala Umar, ya bayyana matsayar UNICEF ne, Alokacin da suka ziyarci Gwamnan Kano a gidan Gwamnatin jahar tare da Kungiyar HILWA , ya jaddada cewa UNICEF da sauran masu ruwa da tsaki karkashin wannan shiri, sun gamsu da irin rawar da Gwamnatin Kano ke takawa na inganta sashen ilimi.
Kungiyar matasan UNICEF ta kunshi mutane 100 da aka zabosu daga Kananan Hukumomi 44 na jahar Kano. Kuma suka samu horo daga Asusun UNICEF a fannin harkar mulki da inganta rayuwar ‘yan kasa da sauran fajjoji. Sannan zasu wayar da kan jama’a kan muhimmancin ilimin yara mata da sashen ilimi baki daya.
Sun kara da cewa “Muna sane da duk kokarin da gwamnatinka keyi, Gwamna Ganduje yana kokarin inganta ilimin ‘ya mace a jahar. Abun da muka zo tattaunawa dakai anan shine batun ilimin ‘ya mace, amma mun fahimta cewa abun ya wuce tunanin mu. Kayi abun azo a gani a wannan fanni, ” cewar Umar.
Itama kungiyar HILWA da Asusun UNICEF ta kafa a a jihohi 14 na yankin arewa Inda aka zabi mata goma goma daga kowacce jaha , ta bakin sakatariyar Kungiyar Ladidi Sani Fagge, ta bayyana cewar an kafasune da nufin inganta ilimin matasa.
Sani Fagge, ta kara da cewa ba a biyan kokarin da matasan keyi na wayar da kan ‘yan uwansu matasa da kuma ilimin ‘ya mace, sai tace hakan abun a yaba musune.
Fagge, ta nuna farin cikinta cewa Kano ta fara gudanar da kudurin da aka sanya a gaba kafin sauran jihohin, wanda tace hakan ya sanya Asusun UNICEF da sauran masu ruwa da tsaki karkashin shirin, yabawa Gwamna Ganduje da ya ayyana bayar da ilimi kyauta ga ‘ya mace da kuma ilimi kyauta a firamare da sakandare.
Duk masu ziyarar, sun gamsu cewa Kano tayi fice a sashen ilimi kan kowacce jaha a tarayyar Najeriya karkashin Gwamna Ganduje, cewar Fagge.
Cikin jawabinsa Gwamna Ganduje, ya tabbatar musu da cewa zaici gaba da ayyukan alkhairi Kamar yadda ya faro a farkon mulkinsa, sai ya kara jaddada cewa, “Da ace abun da mukeyi an faroshi tun shekaru 20 da suka wuce da yanzu labarin yasha banban.”
“Ilimi nauyi ne dake kan kowa. Dole sai an hada hannu, kafin a wayar dakan Al’umma yadda ya dace. Burin mu shine samar da Al’umma tagari, cewar Ganduje.
Gwamna Ganduje zayyana cewa an ware naira biliyan 1.2 don horar da malaman makarantun firamare guda Dubu Ashirin da Biyar da Dari hudu da Tamanin da Shida (25,486),duk da burin magance matsalar rashin kwararrun Malamai tun daga lokacin zangon mulkinsa na farko.
Gwamna Ganduje, ya bayyana lokacin da ya zama Gwamna, ya samu Malamai dubu Ashirin da Biyar 25,000 da basu da takardar izinin koyarwa, don haka sai ya turasu karin karatu.
Da yake magana kan ilimin ‘ya mace kuwa, Gwamna Ganduje, yace gwamnatinsa ta Debi Malamai mata dubu daya da Dari biyar da talatin da tara 1,539 daga Kananan Hukumomi 44 dake jahar, a matsayin wani bangare na samar da aikin yi ga mata da inganta ilimin ‘ya mace.
Gwamnan, ya kara da cewa yana biyan sama da biliyan biyu kudin albashin Malamai Dubu Hamsin 50,000 a jahar domin muhimmancin da ilimi ke dashi.
Gwamnan yace duk da cewa taron anyi shine don ilimin yara daga tushe, amma yayi amfani da damar wajen bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da amincewa da tantance kwasakwasai 66 a kolejin kimiya da kere kere ta Gwamnatin jahar da kuma inganta sauran manyan Makarantu Mallakar jahar.
Gwamna Ganduje, yace ya kafa kwamitin da zai ciyar da ilimi daga tushe gaba a Kananan Hukumomi 44 dake jahar, sai yayi kiran sanya hannun kowa cikin lamarin don cimma burin da aka sanya a gaba.
Ya bayyana cewa an warewa kwamitin, kudi naira miliyan 440 a Matsayin somin tabi, Inda kowacce karamar hukumar ta samu naira miliyan 10 a kason farko.
Ana tsammanin kwamitin zai gyara makarantu guda 490 da azuzzuwa guda 981. Ya bayyana cewa kwamitin ya samar da kujeru 7,915 da kuma kayan koyo da koyarwa a Kananan Hukumomi 44 na jahar Kano.