In Ji Sarki Kano Muhammad Sanusi.
Sarkin Kano Muhammad Sanusi ya ce wajibi ne maganar bada tallafin man fetur da na wutar lantarki su zo karshe. Sarkin ya yi wannan kira ne jiya a Kano, wajen wani taro da aka gudanar na Jamián Ajiya na asusun Gwamnati.
Sarki Muhammad ya cigaba da cewa idan har Gwamnati na bukatar tattalin arzikinmu ya bunkasa, to dole ne ta dauki matakai masu daci saboda a sami cimma nasara.
”Kashi dari na abin da mu ke samu a bangaren man fetur, ana kashe su ne wajen shigo da man fetur. Yanzu kasar nan tana gab da ta durkushe”. In ji Sarkin.
Ya ce ”wai shin menene ke cikin man fetur har da gwamnati za ta yi watsi da batun ilimi, lafiya da kayayyakin ababen more rayuwa sabo shi?’Sarkin ya tambaya.
”Dole ne a shiga cikin yanayi mai wuya kafin a yaki talauci. Ku fada wa mutane gaskiya. Idan farashin man fetur ya tashi a duniya, suma su shirya sayensa da tsada. Idan kuma ya sauko, za su saya da araha. Dole mu shirya wa fuskantar kowane yanayi”, Cewar mai Martaba Sarki.
Sarkin ya ce, alámarin man fetur da kuma wutar lantarki, wani abu ne da ya shafi mutane a daidaikunsu, Don haka bai kamata a ce za a bada tallafin a kansu da sunan yaki da talauci ba.
(Fassara daga Jaridar DAILY TRUST ta yau)