• Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Landan a gobe juma’a
• Femi Adesina ne ya sanar da tafiyan Shugaban kasa Buhari.
•A na saran dawowar shi Nijeriya me a cikin taakiyar makon watan gobe.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Landan a gobe juma’a domin duba lafiyar shi.
Babban maitaimaka masa a kan kafafen yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanar wa da ya fitar a yau Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje zai gina gidajen Malamai guda dubu biyar
Sanarwar ta ce, “Shugaban kasa Buhari zai tafi Landan ranar juma’a 25 ga watan Yunin shekarar 2021, domin duba lafiyar shi”.
Inda kuma ake sa ran dawuwar shi, kasar nan, a cikin mako na biyu, na watan Yuli shekarar 2021″ inji sanarwar