Biafra: Rundunar yan sanda ta kashe wasu da ake zargin yan kungiyar ne
• Har yanzu dai ba a bayyana yawan yan kungiyar da rundunar yan sandan ta kasa ta kashe ba.
• Rundunar dai ta Kai farmakin ne a wasu maboya uku, na wadanda ake zargin yan kungiyar ne.
• “An sami makamai da dama da kuma layoyi a hannun wadan da ake zargin” cewar wani shaidan gani da ido.
A jiya juma’a ce, Rundunar Yan sanda ta kasa, ta kashe wasu da ta ke zargin mambobin kungiyar tada katar baya, da kuma rajin kafa kasar Biafra me, wato IPOB a wani maboyar su da ke jihar Imo.
Samamen da rundunar ta kai a maboyar IPOB da ke yankin Atta da Izombe, da kuma Ideoto na jihar, ta kai shi ne da misali k hiarfe 4 na safe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje ya halarci bikin tunawa da Abiola.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, rundunar IRT, da STS, da rundunar ya ki da garkuwa da mutane ta AKU, da wasu runduna ne,suka kai samamen a maboyar yan kungiyar IPOP.
Wani Shaida ya bayyana wa Jaridar The Nation cewa, lokacin da rundunar ta kai samamen, an Sami bindigu, Motocin sata, abubuwan fashewa, Garin harsashin bindiga, layoyi, wiy-wi, alburusai, da kuma kwayoyin masu sa maye, a hannun wadanda ake zargin yan kungiyar ne.
Duk da cewa dai, ba a bayyana yawan yan kungiyar da rundunar ta kashe ba, amma Shaidan ya ce, “Mafi ya waicin su an kashe su ne a cikin dajin da suke a aboye” inji shi.
Ya kara da cewa, an kama shida daga cikin wadanda ake zargin, inda rundunar yan sanda, ke cigaba da gudanar da bincike.