Ta yaya za’a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya?, Sarkin Musulmai
Mai martaba Sarkin Musulmai Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali shine Kashin bayan cigaba na kowane Al’umma.
KARANTA:-Gwamnatin Jahar Gombe ta karawa Dagatai da Hakimai albashi
Yace “Yan Najeriya dole su fahimci junansu domin rage masifofin dake aukuwa a kasar”
Mai martaba Sarkin Musulmai Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana hakane a wajan kaddamar da Sarakutan Gargajiya na Kabilu daban-daban a Kano.
Kamin Najeriya ta cimma manufofinta, dole kabilu su fahimci junansu.
“Idan akwai fahimta tsakanin kabilun kasar nan to tabbas da akwai cigaba” kamar yadda ya zayyana
Sultan, a jiya lokacin da yaje wajan nadi Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, yace dole shugabanni suyi aiki tukuru don hada kan Al’ummar su, domin da wannan ne zaka samu zaman lafiya zai wanzu a kasar.
Babban matsalar mu a wannan kasar shine rashin fahimtar juna, dazaran mun fahimci juna to zaman lafiya zai wakana
Mu fahimci juna, kada wani ya nuna yafi wani, muna da baiwa daban-daban idan muka hada kai muka kuma fahimci juna to zamu cigaba.