Daga Sabiu Musa Kano
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jahar kano ya jinjinawa hukumar Ta ‘yan sandan yadda suka cafke wadanda sukayi garkuwa da magajin garin daura kuma surukin hadimin Shugaban kasa Muhammad Buhari a samegu dake karamar hukumar kumbotso dake jihar kano.
Gwamnan ya kara da cewa Wannan nasara ce da kuma kara tabbatar da kwarewar su da jarumta inda yace Wannan abun koyi ne ga sauran hukumomin tsoron kasar nan.
Sannan yace abin alfahri ne yadda asirin su ya tonu a jahar kano inda hakan ya kara tabbatar da cewa kano jaha ce mai daukar tsaro da muhimmanci.
A daya bangaren kuma yayi godiya ga Shugaban ‘yan sanda da irin jajircewar sa Wanda hakan yasa aka samu Wannan nasara da kuma Shugaban kasa Muhammad Buhari kan yadda Ko Yaushe bashi da wani abu face ganin an samu tsaro a fadin kasar nan.
Gwamnan yayi godiya ga mazauna yankin inda yace su kara kula da bakin fuska kar su bari a maida yankin mafakar masu aikata laifuka dama jahar kano baki daya, Inji shi.