Wakilinmu shu’aibu Ibrahim Gusau
Wakilai masu aikawa da rahotanni masu zaman kansu sun kauracewa gidan gwamnatin jihar zamfara daga yau.
Hakan ya fitone daga cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Alh. Umar Mahammad Maradun, ya fitar Wanda ke dauke da sa hannun shugaban.
Shugaban ya ce hakan ya farune sakamakon yanda suke samun wulakanci da tozartawa daga jami’an tsaro Koda sun bada katin sheda ta wurin aikinsu.
Jami’an tsaron dai sukan nuna halin ba sani ba sabo tare da rashin mutunta umarnin DG press da SA media, idan suka bada na cewa, a barka ka wuce.
Alh. Umar, ya Kara ds cewa membobin zasu dakata daga shiga gidan gwamnati da Kuma dakatar da tura duk wani abu da ya shafi labarin Gwamnatin har sai an daidaita.