A kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi na bunkasa tattalin arziki da kara samar da zaman lafiya, Gwamna Malam Nasir Ahmed El-Rufai yau ya aza harsashin ginin sabuwar kasuwa ta zamani a garin Kasuwan Magani da ke Karamar Hukumar Kajuru. Wannan wani yinkuri ne da zai taimaka wurin samar da zaman lafiya da bunkasa tattalin arziki a wuraren da aka yi fama da rikice- rikice na addini da kabilanci..
Kasuwar Magani ta sha fama da rikice rikice a baya. Na kwanan shi ne na shekara ta 2018 wanda ya yi sanadiyar konewar kasuwar baki daya. A baya Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana shirinta na gyarawa da bunkasa kasuwannin da suka lalace kamarsu, Kasuwar Zonkwa, Kasuwar Magani da sauransu.
A yau Laraba ne, Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin shirinta na zamanantar da kasuwanni ta aza harsashin ginin konanniyar Kasuwar Magani saboda ta bunkasa tattalin arziki da kuma ba kowa dama na mallakar shaguna a kasuwan domin samar da zaman lafiya.
Wannan sabuwar kasuwan da za a gina a Kasuwar Maganin za ta kunshi shaguna 2,024 da mahauta da ofishin ‘yan sanda da karamin asibiti da yankin kashe gobara da sauransu.
Gwamna Malam Nasir Ahmed El-Rufai a jawabinsa ya roki al’umma su zauna lafiya. “ina rokon al’umma su zauna lafiya da juna domin a sami dawwamammiyar zaman lafiya. Cigaban kowace al’umma yana bukatar kyakkyawan yanayi wanda kowane mutum zai ji yana rayuwa ba wata fargaba. Mu hadu mu yaki talauci tare da ku domin samar da dawwamammen zaman lafiya.”
Bugu da kari, Gwamnan ya bayyana aniyar gwamnati na taimaka wa ‘yan kasuwa domin su mallaki shuguna. “Ga ‘yan kasuwa da sauran masu sha’awan sayen shaguna a kasuwan gwamnati ta fito da wani shiri domin a taimaka musu da kudi a wani shiri na hadin gwiwa tsakanin Hukumar Kula da Kasuwanni da kuma Bankin Sterlin domin samar musu da bashi.”, Inji Malam Nasir Ahmed El-Rufai.