Wasu daga cikin iyayen daliban da akai garkuwa dasu a makarantar sakandire dake Yawuri jahar Kebbi, sunce “Yan bindigan sun turo mana bidiyon yadda suka aurar da yaranmu.” Kamar yadda Jaridar Dailytrust ta wallafa
Yau kimanin sati biyu kenan da yin garkuwa da Daliban makarantar sakandire dake Yawuri Jahar kebbi.
Daya daga cikin iyayen yace a duk lokacin da suka kira ma su garkuwa da Mutanen sukan ce musu yaransu suna lafiya.
“Yan bindigan dai cewa sukai bazasu sasanta da iyayen ba sai dai da gwamnati.”
KARANTA:- Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Kajuru, da wasu Mutum 13
“Wani lokacin sukan Kira su, su hadasu da yaransu su gaisa idan yaran ya rike lamabar iyayenshi a Kai, amma ni har yanzu ban taba gaisawa da yaran nawa ba.” Kamar yadda ya shaidawa Jaridar BBC.
Ya cigaba da cewa “Tunda aka dauke yaran, yara goma ne kacal sukayi waya da iyayensu.”
“Wasu daga cikin iyayen yaran sun zauna tare da gwamanatin jahar Kebbin, Iyaka dai gwamnatin ta nuna bacin ranta kan aukuwar lamarin, tace za’a dauki mataki amma Yau kimanin sati biyu kenan ba abunda ya faru.” Yace.
Yace “yanzun dai muna cikin zaman dar-dar kuma gashi Sallar Idi na karatowa.”
“Dayawa mutane suna zaune da iyalansu lafiya mu kan kullun cikin bakin ciki.”
Daga karshen ya roki gwamnati data kara himma don kwato yaransu ko zasu samu zaman lafiya.
Comments 1