Yan bindiga sun yi garkuwa da Mai Martaba sarkin Kajuru, da wa su iyalan shi goma sha uku.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa, wani bafade a fadar Mai maitaban, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari.
An yi awon gaba da Sarkin ne, tare da Matan shi guda Uku, da jikokin shi biyu, da kuma wasu masu taimakama shi Uku, sai wasu mutane biyar dake yankin.
A cewar shaidan ” Kwana daya kacal bayan Sarkin ya shirya Taron kan lamarin tsaro a yankin, biyo bayan wani rahoton barazanar yin garkuwa da shi da aka samu, wanda abun takaici hukumomin tsaro ba su maida wa yan bindigan martani ba” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi garkuwa da kananan Yara a Sabon Gari
Wannan na zuwa ne, a dai dai lokacin da yan bindiga ke tsaka da cin karansu babu babbaka, a ciki da wajan jihar Kaduna, inda su ke yin garkuwa da mutane, domin ammasan kudin fansa.