Gwamnatin tarayya ta sanar da Talata 20 ga watan July, da kuma Laraba 21 ga watan July, 2021 a matsayin ranakun hutun don gudanar da shagulgulan Sallah.
Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola, shine ya sanar da haka a matsayin wakilin gwamnatin tarayya, ya Kuma taya Musulmai murnar Sallah, gami da fatan gudanar da shagulgulan Sallah lami lafiya. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta wallafa a shafinta
Rauf Aregbesola yace ” Ina Kira ga Musulmai dasu cigaba da ya da kauna, tausayi da kulawa kamar yadda Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W) ya koyar, ya kuma kiraga Musulmai da suyi amfani da wannan lokacin wajan yima Kasa addu’oi na zaman lafiya da hadin kai a kasar nan, duba da yanayin hali na tsaro da muke fuskanta a wannan lokacin, a Arewacin Najeriya Bokoharam, a Yammacin Najeriya masu garkuwa da mutane, sannan a kudanci Najeriya kuma masu fafutukar kafa kasar Oduduwa da Biafra.”
Gaskiyar Lamari: Sakamakon Gwajin Lafiyar Muhuyi Magaji, ya zo da alamar tambaya
Ministan ya kuma bayyanawa Mutane cewar, gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari na iya kokarin ta wajan Kawo karshen ta’addanci dake Kasar nan, da kuma tabbatar da kare rayukan Yan Najeriya, tare da fito da hanyoyi tayadda mutane za su samu abunyi, da kuma samar da abinci a makarantu gami da tabbatar da tsaro a cikin makarantun kasar nan, duba da irin yadda yan ta’adda ke kai farmaki a makarantu.”
Rauf Aregbesola lokacin da yake taya Musulmai murnar Sallah ya shawace su da su kai rahotan duk mutumin da basu yadda dashi ba, ko wani ta’addanci daka iya faruwa yayin bikin Sallah.
Ya kuma jawo hankalin mutane da su cigaba da tsare dokar cutar Covid-19 yayin gudanar da shagulgulan Sallah, a cigaba da amfani da takunkumi, a bada tazara a kuma cigaba da wanke hannu, dole mu cigaba da daukan alhaki cikin dukkan bukukuwan da za su gudana a cikin shekara.
Ministan ya kuma jajantawa iyalan da yaransu ke wajan masu garkuwa da mutane, da kuma wadanda ke cikin kunci, muna cigaba da yi muku addu’a a cikin zukatanmu. Kamar yadda yace.