• Sakamakon Gwajin Lafiyar Muhuyi Magaji, ya zo da alamar tambaya.
• Sakamakon Gwajin da Muhuyi ya gabatar Bai dauke da lambobin da su ka dace.
• Hakan na nuna cewa, da yuwuwar Gwajin na bogi ne.
Sakamakon lafiyar dakataccen Shugaban hukumar amsan korafe-korafen al’uma, da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano Muhuyi Magaji, da ya mika wa kwamitin wucin gadi dake binciken shi a kan wasu zarge-zarge, ya nuna akwai alamomin tambaya da suke bukatar amsa.
Jaridar SAHELLIAN TIMES ta ruwaito cewa, ta yi dubi na tsanaki, a kan sakamakon da ke dauke da bayanan lafiyar Muhyi, kamar yadda ya dace.
Jaridar ta ce, Fom din bai dauke da Lambar Asibiti kuma bai dauke da Lambar dakin Gwaji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalissar Dattijai ta sake amince wa da wani Kwamishinan Hukumar INEC
Sabida rashin wadan nan lambobin biyu, ba bu wanda zai iya binciko sakamakon wannan gwaji, a Babban Asibitin kasa dake birnin tarayya Abuja.
A fadin duniya baki daya, kowa yasan cewa, ba bu wani dakin waji, da zai yi gwaji batare da ya sanya wa gwajin lambar shi ba, rashi wadannan lambobin a jikin Fom din, na nuna cewa, watakila gwajin na bogi ne.
Kazalika ranar daukan waji da kuma ranar fitar da sakamakon ya nuna cewa, a rana guda aka yi su. (12/07/2021).
Kuma akalla gwajin Stool da a kayi wa Muhuyi, a kan sami tazarar awa 48 kafin fitowar sakamakon gwajin.
Shi kuma sakamakon da Muhyi ya gabatar ya nuna cewa, a ranar da akai gwajin kuma a ranar a kasami fitowar sakamako.
Irin wannan binciken na da da, kawo matsalolin da ake samu a harkan kiwon lafiya, inda ake dada samun bayanan asibiti na bogi.
Bugu daka ri, sakamakon ya nuna cewar, rubutun ne man bukatar yin wajin, da kuma rubutun sakamakon, sun yin kamai ce-ce-niya da juna
Hakan ya nuna cewar, Mutum daya ne ya rubuta bayanan sakamakon, wadan da ya yi sojan gona a matsayin likita.