• Wata Kotu a jihar Akwa Ibom ta yanke Hukuncin kisa ga yan sanda biyu.
• Kana hukuncin zai shafi wasu Mutum uku dake aiki tare da wadannan jami’an yansanda.
• Hakan ya kawo karshen zaman sauraron karan har na tsawon shekara 10.
Bababn Kotun jihar Akwa Ibom dake zaman ta a karamar hukumar Ekpene ta yanke wa wasu jami’an yan sanda biyu, da kuma wasu mutun uku hukuncin kisa.
An yankewa mutannan ne hukuncin a yau juma’a, bisa laifin garkuwa da wani Dilan Shanu Mai suna Alhaji Muhammad Barkindo, a garin Uyo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Niger ya amince da hukuncin kisa kan masu Garkuwa da mutane
A lokacin da ta ke yanke hukuncin, Mai shari’ar Kotun Eno Isangedighi ta ce, wadanda ake zargin sun amsa laifin su, inda kuma ta roki Allah da ya gafarta musu.
“An kama jami’an ne bisa zargin garkuwa da Alhaji Muhammad Umar a ranar 25 ga watan Nuwanban shekarar 2011, inda daga bisani suka amsa laifin su, Kuma aka yanke musu hukuncin kisa, bisa sashin doka na daya , biyu cikin baka, na kundun tsarin dokar jihar Akwa Ibom na shekarar 2009” a cewar Mai shari’ar.
Jami’an yan sandan sun hada da, Kofur Friday Ido da Kofur Saturday Okorie, wadanda Yan a salin garin Ikot Inyang da Ikot Etenge ne dukkannin su, su na zauna ne a karamar hukumar Oruk Wanda tuni rundunar Yan sandan Nigeria ta sallami su daga bakin aiki.
Sauran mutanan da aka yanke wa hukuncin kisan sun hada da, Walter Jack Ido, da Ido Okon Etim mazauna garin Nsit, sai Ikot Asua dake zaune a Karamar hukumar Nsit Atai na jihar
An dai yi amfani da gidan Udo Okon Etim ne, wurin boye Wanda aka kayi garkuwa da shi, inda su ka bukaci Naira milliyan dari, a matsayin kudin fansa.
Hukuncin da Kotun ta yanke ya kawo karshen zaman jiran sauraran karan, na tsawon shekara 10, bisa zargin mutanan, da su ke da hannu wurin garkuwa da wani nasani a fannin kiwon lafiya na jami’ar Uyo, Mai suna Dakta In Enang a watan Ogustan shekarar 2011.