• Jami’an tsaro sun yi awon gaba da Sheikh Abduljabbar.
• Ana dai zargin Abduljabbar ne da yin kalaman batan cinkan fiyayyan halitta Annabi Muhammad S..A.W.
• Kafin kamashi dai sai da gwamnatin jihar ta shirya Mukabala amakwan da ya gabata da Abduljabbar da wasu malaman jihar.
Wasu rahotanni daga jihar Kano na nuni da cewar Yansanda a yammacin ranar Juma’a sun yi awon gaba da Abduljabar Nasiru Kabara dake unguwar Filin mushe a yankin karamar hukumar Gwale.
Idan baku manta ba, a makon da ya gabata aka gudanar da wata mukabala tsakanin Abduljabar da Malaman Kano inda aka zargi Abduljabar da yin kalaman batanci ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam zargin da shi Abduljabar ya kasa karewa.
Bayan kammala waccan mukabalar Abduljabar ya bayar da wata sanarwa, inda yace ya janye dukkan kalaman da ake zargin yayi, yana mai baiwa al’umma hakuri, daga bisani kuma ya janye wannan tuban da yayi.
Tuni dai akai ta kiraye kirayen Gwamnatin Kano ta dauki mataki akansa ko kuma ya fuskanci fushin mutane.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukuncin kisa ta tabbatar ga jami’an yan sanda biyu a jihar Akwa Ibom
Sai dai wasu rahotanni sun nuna an cafke Abduljabar a yammacin wannan rana.
Haka Zalika, an kaishi kotu ne, Kuma a yau Kotun ta bada umarnin a kaishi gidan Gyaran Hali, a yayinda ake cigaba da Shari’ar shi
Comments 1