Wakilinmu Ahamed Musa Gumel
Hukumar bada katin dan kasa a jihar Jigawa ta ce mutane dubu dari biyar da sittin da biyar ne kacal daga cikin mutane miliyan biyar da dubu dari hudu suka yi rijistar katin ya zuwa yanzu a jihar nan.
Babban jami’in Hukumar a Jihar Jigawa, Malam Aminu Jakada ya bayyana hakan ga wakilinmu a Dutse
Malam Aminu Jakada ya ce adadin wadanda suka yi rijistar bai fi kashi goma cikin dari ba, na yawan al’ummar Jihar Jigawa.
Ya jaddada bukatar al’ummar Jihar nan su tashi tsaye domin yin rijistar katin dan kasa bisa la’akari da sauye-sauyen zamani, inda ya ce a yanzu haka akwai cibiyoyin yin rijistar katin sama da arba’in a fadin Jihar nan.
Babban jami’in ya kara da cewa mallakar katin ga kowane Dan Najeriya na da muhimmanci sosai, don haka akwai bukatar kowa ya mallake shi.
Malam Aminu Jakada wanda ya yabawa Mai Martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussain Adamu da kungiyar Hadejia INA -MAFITA tare da sauran kungiyoyin bisa gudummawar da suke baiwa Hukumar, ya jaddada kudirin Hukumar na hada hannu da masu ruwa da tsaki wajen ganin yan Jihar Jigawa ba a barsu a baya ba wajen mallakar katin.