Daga: Comrd. Haruna Sardauna.
Domin raya karkara ta fuskar samar da ingantaccen kiwon lafiya a al’ummah mazauna kauyika, gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, yayi alwashin samar da kananan asabiti adadin yawan Guduma 174 dake fadin jihar Yobe.
Gwamna Mai Mala Buni, ya bayyana kudirin sa na samar da kananan Asabiti 174, a jawabin shi na ranar rantsuwa a matsayin Gwamnan dazai mulki jihar Yobe, wannan kudiri zai taimakawa mazauna karkara, musamman ma mata masu juna, wanda suke samun matsalar Borin Haifuwa ko yoyon jini.
Iyaye mata a kauyika suna fuskantar matsalar Borin Haifuwa ko zuban jini, matsalar da ake fuskanta kafin a kawo Mai Haifuwa zuwa Asibiti gari domin a ceto rayuwar uwa da dan dake cikin ta, wani lokacin sai rai yayi halinsa saboda rashin samun ceton gaggawa, sau tari akan iya rasa uwar da dan cikinta saboda rashin samun ceton Ingozoma akan lokaci.
Wannan dalilin ne yasa, gwamna Mai Mala Buni, yayi alwashin gudanar da wannan kudirin, da manufar rage yawan mutuwan mata a gurin Haifuwa, rayuwar mazauna Karkara zai inganta, kasancewar lafiya itace ginshikin rayuwa kuma itace al’ummah sukafi bukata a kusa da su, saida lafiya komai dazai tafi yadda ya dace.
Samar da ingantaccen kiwon lafiya a talakawa mazauna karkara, yana sahun gaba, manyan aiyukan da bakauye yake bukata shine, kiwon lafiya, wutar lantarki, hanyoyin maraya da tacaccen ruwan sha.
Cikakken Goyon bayan da adu’ar alherin Talakawan Yobe, shine zai baiwa mai girma Gwamna Mai Mala Buni, karfin guiwar gudanar da wannan mahimmin aiki na samar da ingantaccen kiwon lafiya a Talakawa mazauna karkara.