• Gwamnatin Zamfara ta bai wa iyalan jami’an yansandan da aka kashe, Naira milliyan 15.
• Iyalan kowani Wani Mamaci zasu sami naira milliyan daya, inda wadanda suka sami raunkiga zasu sami naira milliyan biyu.
• Kwamishinan Yada labarai na jihar Zamfara me ya bayyana hakan a garin Gusau.
Gwamnan jihar Zamfara ya bai wa ilayan jami’an rundunar yan sanda da aka kashe Naira milliyan 15, wani harin kwantan bauna a makon jiya, a garin Korar Mota dake karamar hukumar Bungulu ta jihar.
Kwamishinan yada labarai Ibrahim Magaji Dosara ne ya bayyana hakan a yau juma’a, a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Gusau.
A cewar sanarwar dukkanin iyalan Mamaci daya zasu sami naira milliyan daya, ya yin da iyalan wadanda su ka sami mummunan raunika zasu sami naira milliyan 2, duk da cewa, gwamnan jihar ya dauki nauyin kula da lafiyar su.
Sanarwar ta kara da cewa, Gwamnan Bello Muhammed Matawalle ya ce, hakan na daya daga cikin alkawarin da ya dauka na tallafa wa iyalan jami’an tsaro na-gari, da su ka rasa rayukan su sanadiyar kare rayuka da dukiyoyin al’uma.
“Tun bayan hawan shi garagar Mulki, Gwamna Matawalle ya na da dangantaka Mai kyau da hukumomin tsaro, kuma gwamnatin shi na tallafa wa hukumomin tsaro, domin sauke nauyin da ya rataya awuyan su” inji sanarwar.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kama Mutane biyar da zargin yin Luwadi a Kano
Gwamna Matawalle ya ziyarci wadanda su ka sami raunika a asibiti domin jajantamasu, bisa hadarin da ya afku dasu.
Comments 1