Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya bai wa Paris Saint German Fam milliyan 102, domin ganin ta kammala shiyan Kylian Mbappe.
Haryanzu dan wasan gaban, ya gaza sadaukar da rayuwar shi ta kwallo a Parc Des Princes, Wanda kwantiragin shi a kungiyar zai kare nan da shekarar 2022. Kuma hakan yasa Kocin kungiyar Mauricio Pochettino ke wani hali na rasa dan wasan nan da watanni 12 masu zuwa, ba tare da samun ko si-si ba.
Sai dai kungiyar ta PSG na da kwarin gwuiwar ce, zuwan Lionel Messi kungiyar ka iya janyo ra’ayin Mbappe, wurin kulla sabon yargegeniya da kungiyar da ke babban birnin Faransa.
A cewar wani Dan jarida Mai suna Paco Jo Delgado, Real Madrid ta shirya Mika wani tayi Mai gwabi ga PSG, domin ganin ta kammala siyan Mbappe a kakan wasan nan da muke ciki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar yan sanda ta tabbatar da kashe Manoma a Kaduna
Delgado ya kuma ce, a kwai yuwuwar Mbappe ya koma Madrid nn da kakar wasa Mai zuwa, batare da ko si-si ba, muddun PSG ta ki amince wa da tayin da Real Madrid za ta yi mata.
Sai dai ana ganin cewa, Dan Kasar Faransa zai zauna da mahukunta kungiyar ta PSG a gobe Litinin, domin sanin makomar shi a kungiyar.
Mbappe ya ci wa kungiyar ta PSG kwallaye 132 a cikin wasanni 172 da ya fafata mata, inda kuma ko a makon nan, ya tallafa wa takwaran shi Mauro Icardi, ya ciwa kungiyar wallon da ya bata nasara a wasan ta, na gasar Ligue 1 da Troyes