Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya mika sunayen mutane 17 ga majalissar Dokokin jihar, domin tantance su a matsayin Kwamishinoni.
Hakan na zuwa ne watanni kadan, bayan da Gwamnan jihar ya yi garan bawul a makarraban sa, inda ya kori sakataran gwamnatin jihar, Shugaban Ma’aikatan fadar gwamnantin jihar, da kuma wasu mambobin majalissar zartarwar shi.
Mai Magana da yawun kakakin majalissar Dokokin jihar Abdul Ahmed Burra ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanar wa da fitar a jiya Talata.
Sunayen da aka fitar kuma jaridar Dimokuradiyya ta gani, sun kunshi sunayen wasu tsaffin Kwamishinoni da sabbin daga dukkannin kananan hukumomi ashirin dake jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar yan sandan jihar Delta ta kama Barayin mota guda 11
Wadanda sunayen su yafara fito wa akawai: Abdulrazak Nuhu Zaki, Aliyu Usman Tilde, Hamisu Mu’azu Shira, Hajara Gidado, Asma’u Ahmed Giade, Maryam Bagel, Garba Dahiru, Nurudeen Abdulhamid da kuma Usman Abdulkadir Moddibo.
Sauran sunayen sun hada da Abubakar Abdulhamid Bununu, Sama’ila Burga, Aminu Hammayo, Sama’ila Dahuwa Kaila, Umar Babayo Kesa, Dayyabu Ciroma, Ahmed Aliyu Jalam da kuma Abdulkadir Ibrahim.