Jami’an yan sanda a jihar Delta, sun kama wasu mutane 11 da suke zargin yan kungiyar asiri ne, fashi da makami, kwacen Mota da kuma kisan mutane daban daban a fadin jihar.
A cikin wata sanar wa da Kwamishinan yan sandan jihar Air Mohammed Ali ya sanya wa hannu, Kuma ya bai wa kafafen yada labarai, ta bayyana cewa, jami’ai na musamman dake yaki da Yan kungiyar asiri, sun sami labarin cewa, wasu da ake kyautata zaton yan fashi da makami ne, da kuma Garkuwa da mutane suna aikin ta’addancin yankin Ogorode na garin Sapele a jihar.
A cewar sanar war, jami’an yan sanda suka isa wurin, sun kama Mutane biyar da ake zargin, Nelson Ofurhie Mai shekara 40, Efe Adams Mai shekara 32, Williams Onufuevue Mai shekara 46, Enajitu Itiefie Mai shekara 37, da kuma Ohhenero Eruteta Mai shekara 37.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun farmaki wani yanki a Katsina
Abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindiga kirar AK 47 guda daya, harsasai arba’in da bakwai mai girman 7.62mm, wasu muggan magunguna masu ƙarfi, da Mota kirar Mercedes Benz Jeep reg. Mai dauke da Lamba:. AFZ 735 HW, da farar Lexus Jeep Mai lamba: KUJ 983 NW da dai sauransu su.
Kazalika sanar war ta bayyana cewa, caji ofishin din yan sanda dake garin Asaba, sun kama sauran wadanda ake zargin ne a Otel din Elemedo, lokacin da suke gudanar da bincike.
Comments 1