Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta miki cek din kudi na naira milliyan 6 da dubu dari 9 ga iyalai 12 na jami’an ta, da su ka rasa rayukansu, sanadiyar kare martabar kasar nan.
Kwamishinan yan sanda na jihar Musa Baba ne ya miki cek din ga iyalan a shalkwatar rundunar, kamar yadda Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Nafi’u Abubakar ya fitar da wata sanarwa a yau Litinin, a Birnin Kebbi.
A cikin sanarwar da ya fitar a yau Litinin, Kwamishinan yan sandan jihar ya ce, an dauki wannan matakin ne badon tallafa wa iyalan mamatan kadai ba, face harda kara karfafawa sauran jami’ai gwuiwa kan ai kin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an soji sun kubutar da mutune 15 a Kaduna
Sanarwar ta yi nuni dacewa, ” A madadin Shugaban rundunar yan sanda na kasa Usman Baba Alkali, Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi Alhaji Musa Baba ya miki cek din naira milliyan shida da dubu dari Tara ga iyalai 12 na jami’an yan sandan da suka mutu, domin kare kasar mu ta gado”.
Kazalika sanar war ta kuma shawarci wadanda suka amfana da su yi amfani da kudaden kamar yadda ya dace.
Har’ilayau sanarwar tace, iyalan da su ka amfana sun kasan ce cikin murna bayan mika musu cek din, inda kuma suka yaba wa Shugaban rundunar yan sandan na kasa.
A karshe iyalan sun kuma roki Allah madaukakin sarki da ya ci gaba da kare shi, da kuma tallafa miki a rayuwar sa baki daya.