By Ishaq Dabai
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya yi watsi da umarnin Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
A wata sanarwa da Gwamnan ya fitar ta hannun Kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba, a ranar 16 ga watan Agustan da ya gabata.
Gwamnan ya umarci mutane da su yi watsi da wani rahoto da aka riƙa yaɗawa, cewa matar Gwamna Dr. Hafsat Abdullahi Ganduje ta ayyana wanda zai gaji kujerar Gwamna.
Sai dai abin mamaki shi ne yadda aka hango shugaban jam’iyyar a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, yana musanta sanarwar da Gwamnan ya bayar.
Abdullahi Abbas ya ce, ba sa tare da waccan sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai ya fitar a madadin Gwamna.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake ganin shugaban jam’iyyar na wuce gona da iri wajen sakin zance ba sakakaba.
Ko a kwanakin baya Gwamnan Ganduje yayi Alla-wadai da masu yaɗa kalamai marasa daɗi na tunzura jama’a da sunan siyasa.
Masu bibiyar al’amuran siyasar Kano dai na ganin cewa, wannan koma baya ne ga jam’iyyar ta APC, idan har shugabanta zai riƙa bijirewa Gwamna, Ko kuma ya riƙa ƙoƙarin yin abin da zai kawo rabuwar kai tsakanin ƴaƴan jam’iyyar maimakon haɗin kai.
A waccan sanarwa dai Gwamna Ganduje ya fito ƙarara ya bayyana cewa, ba a yiwa mai ɗakinsa kyakkyawar fahimta ba, kuma a yanzu babu wani da aka ce shi ne ɗan takara, Hassalima Gwamnan ya mayar da hankali ne wajen yin ayyukan raya ƙasa ga jama’ar Kano.
Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa, wasu marasa kishin jam’iyyar ne kawai suka riƙa yaɗa labarin da zummar kawo rarrabuwar kai.