By Ishaq Dabai
Matar da ake zargi da satar jarirai a Asibitin Murtala dake jihar Kano mai suna Hassana Abubakar ta musantan zargin da ake yi mata na satar jarirai, inda ta ce aikin likitanci ne ya kawo ta jihar kano daga Bauchi.
Hassana ta ce dalilin shigar ta wannan asibiti taje ne wajan yayan ta da zummar ta karbi lambar wayar malamin su, mai suna Sale domin ta shigar da korafi bayan da takardun makarantar ta da (I.D card) suka kone a hatsarin mota akan hanyar ta, ta zuwa Kano.
Kuma yayan nata shine wanda yace kar ta tsaya a ko’ina sai ta je sashin kula da haihuwar jarirai na asibin sai yazo ya same ta, daga nan ne sai rashin fahimta ya shiga tsakanin su da wata mata kuma a wajan aka fara ce mata satar yara tazo yi a sibitin.
A yayin da Jaridar Dimokuradiyya take zantawa da matar wadda take hannun jami’an tsaro a yanzu haka, domin gudanar da bincike, ta kara da cewar, ta yi duk mai yiwuwa wajen kiran wayar yayan nata amma wayar sa taki tafiya.