Yan wasan irin su Alison Becker, Fabinho, Roberto Firmino, Gabriel Jesus, Ederson da kuma Fred ba za su sami damar taka Leda ba, a wasan da kungiyoyin su za su buga a karshen makon nan, na gasar Firimiyar Kasar England
Kungiyoyin da wannan lamari zai shafa sun hada da Liverpool, Lead United, Manchester City da kuma Manchester United, inda wadannan kungiyoyin za su ka ra a wasannin karshen makon nan batare da yan wasan kasar Brazil ba, Saka makon sa’insan dake tsakanin hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, da kuma takwararta ta kasar Brazil.
Jaridar Goal.com ta ruwaito cewa, Hukumar FIFA ta tabbatar da wajabta wa kungiyoyin gasar Firimiya killace yan wasan Brazil na kwanaki biyar, kamar yadda Hukumar kula da kwallon kafar kasar Brazil din ta tilasta a kasar ta.
Wanda hakan ne ya sa yan wasa 8 na kasar Brazil dake taka leda a kungiyuyi daban-daban na gasar Firimiya, ba za su samu damar taka Leda ba, a karshen makon nan.
Yan wasan Liverpool guda uku Alisson Becker, Fabinho da Roberto Firmino, da kuma yan wasan Manchester City Gabriel Jesus, da Ederson, sai dan wasan Manchester United Fred, da tauraron kungiyar kwallon kafa ta Leeds United Raphinha.
Kazalika hukumar ta gargadi kungiyoyin da cewa, za su fuskanci hukuncin daka iya hada wa da haramta musu buga wasannin, idan suka ki bin umarnin ta.