Rufe kasuwanni a fadin Arewacin Nigeria ya fara zama barazana ga yan bindiga a shiyyar Arewacin Nigeria. Akalla gwamoninin jihohi hudu ne suka rufe kasuwannin jihohinsu, domin kawo karshen ta’addanci.
Kwanaki kadan bayan rufe kasuwanni a wasu garuruwa na jihar Sokoto, yan bindiga sun fara tambayar kayan abinci a matsayin kudin fansar sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Wani mazaunin Sabon Birni, wanda ya bukaci a sakaya sunanshi ya shaidawa manema labarai yadda yaron wani makwafcinsa ya samu yanci bayan da suka kaiwa ‘yan bindigar kayan abinci.
“Sun yi garkuwa da diyar wani mazaunin kauyenmu, kuma muka gaza hada kudin fansar, daga bisani suka ce mu kai masu kwano 10 na shinkafa domin karbar yarinyar, kuma sun cika alkawarin su.”
KARANTA WANNAN: Kano: An Cafke Matar Da Ta Saci Jariri A Asibitin Nasarawa.
Haka shi ma wani mazaunin jihar Sokoto, ya shaidawa jaridar Daily Trust yadda yan bindigar suka bukaci kayan abinci da kuma lemuka domin sakin wani direba da suka yi garkuwa da shi.
“Da farko sun bukaci mu kai masu miliyan sha biyar, kafin daga bisani suka amince mu kai masu dubu dari shida.
“Sun bukaci mai gidansa wanda ni abokina ne cewar ya yi amfani da kudin ya sayo masu buhunan shinkafa, lemu na kamfanin Fearless, katon katon na taliyar spaghetti, sigari da kuma kai masu sauran canjin. Har yanzu abokin nawa yana kokarin hada kudin,” a cewar sa.
Wani mai fashin baki kan harkokin tsaro, Aminu Bala Sokoto (mai ritaya), ya shaida cewa shigo da jami’an soji a cikin jihar Zamfara don yaki da yan bindiga na haifar da d’a mai ido.