Babban Hafsan Sojojin Nigeria COAS, Faruk Yahaya, ya ce, za su yi wa yan tada kayar baya, da suka hadar da Yan bindiga da masu garkuwa da mutane “ yaren da suke fahimta. ”
Ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin da babban hafsan sojan yake jawabi a wani taro da ya gudana a Babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban sojin na wannan batu ne yayin da ake samun karuwar hare -haren yan bindiga a fadin kasar, wanda ke haddasa kashe -kashe da garkuwa da mutane.
Yahaya ya ce, jami’an sojoji na ci gaba da jajirce wa kan aikinsu, na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin Nigeria.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta aike da wadanda suka kashe Musulmi a Osun gidan gyaran Hali
Kazalika majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Yahaya ya ce, “Ina so in yi amfani da wannan damar in shawarci wadanda ke rura wutar rikicin da ake gani a fadin kasar nan, da su guji ayyukan rashin kishin kasa, yayin da muke jajirce wa, wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya a kowane bangare na kasar nan, cikin kankanin lokaci,”
A wani laabrin Kuma na daban.
Rundunar yan sandan Nigeria za ta dauki Sabin jami’ai guda 60,000, a cikin shekaru shida masu zuwa.
Babban sufeton yan sandan Nigeria IGP Usman Baba ne ya bayyana hakan, a yau Laraba yayin ziyarar aiki da ya kai ga rundunar yan sandan jihar Kwara a Ilorin, babban birnin jihar.
Wannan shi ne daidai lokacin da shugaban yan sandan ya bayyana Kwara a matsayin jiha mafi zaman lafiya a fadin kasar nan, idan aka kwatanta da sauran jihoh dake Nigeria.
Kazalika sifecton ya ce, rundunar yan sandan za ta dauki sabbin jami’ai akalla 10,000 a kowace shekara, har na tsawon shekaru shida.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya ba mu izini mu dauki jami’an‘ yan sanda 10,000 a kowace shekara, har na tsawon shekaru shida masu zuwa nan gaba. Kuma Mun fara amma ba mu yi ba a shekarar 2020. Don haka, za mu dauki na shekarar 2020 da 2021 tsakanin yanzu zuwa nan dan karshen shekara nan. Inda za su sami horo na tsawan watanni shida. Don haka Muna saran nan da zuwa karshen shekarar 2021, za mu Sami Karin jami’ai 20,000 a cikin rundunar Yan sanda ”inji Baba.
Ya kara da cewa za a dauki sabbin jami’an ne daga kananan hukumomi 774 dake fadin kasar nan, inda ya kara da cewa, bayan kammala horas da su, a na duba yuwuwar tura jami’an zuwa jihohin su na asali domin bada gudun mawa wajan wanzar da zaman lafiya a Nigeria.
Tun da farko, a nasa jawabin, Kwamishinan yan sandan jihar Kwara, Mr Tuesday Assayomo ya ce, rundunar yan sandan jihar, ta na fama da karancin jami’ai, inda take da jami’an yan sanda Maza guda 3,500 kacal.