By Ishaq Dabai
Jami’an da ke aiki da tawagar masu sintiri da aikata laifuka na Rundunar ‘J’ Command Elemoro sun cafke wani da ake zargi da fashi da makami da kuma karin wani da ake zargi ‘yan kungiyar asiri ne da bindigar ganga guda biyu a cikin gida da harsasai guda uku.
Wanda ake zargi da fashi da makamin mai suna Alabi Timothy mai shekaru 23, an kama shi ne da misalin karfe 12:30 na safe a General Paint, unguwar Garden, Lekki a lokacin da ‘yan sanda ke tsayar da ababen hawa a shingen bincike.
Rahontanni sun bayyana cewa an samu bindigogi biyu na gida da harsasai guda biyu ciki har da harsashi mai tsada da aka boye a cikin jakar dake hannun Timothy, inda yake zaune a titin Baale Majek Ajah.
Kazalika, an kama wani dan kungiyar asiri, Badmus Toheed dan shekara 22, dan kungiyar asiri ta Aye Confraternity dake unguwar General Paint ghetto, Ajah da misalin karfe 12:45 na safe, Badmus Toheed ya yi ikirarin cewa an shigar da shi cikin kungiyar ta Aye Confraternity tun a watan Yuni 2021,A wani labarin mai kama da wannan, an cafke mutum biyu da ake tuhuma da bayar da cin hanci ga jami’an ‘yan sanda don ganin an saki mutanen biyu da kuma gurbata shari’a da ake yi musu.
Yayin da wani mai sina Adariku mai shekaru 34, mazaunin gida mai lamba 66, dake Henry Smith Close, dake unguwar Abidjan, Ajah ya bayar da cin hancin na naira 400,000 a cikin tsabar kudi don a saki wanda ake zargi da fashi da makami mai suna Folorunso Akeem mai shekaru 43, inda ya yi tayin bada tsabar kudi naira 100,000 don tabbatar da an saki wanda ake zargi dan kungiyar asiri.
Da yake tabbatar da kamun masu laifin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas CSP Adekunle Ajisebutu ya ce,“ ya kuduri aniyar tabbatar da adalci ta hanyar bincike mai zurfi, ga jami’an ‘yan sandan da ba su yi kasa a gwiwa ba wajen kin karbar cin hanci”, Sai dai kuma Odumosu ya bayar da umurnin a mayar da shari’ar zuwa Kwamitin dabara na rundunar don ci gaba da bincike da gurfanar da shi.