By Ishaq Dabai
Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur DPR, a Abuja, a ranar Alhamis ta rufe kamfanonin gas 11 da gidajen mai guda biyu wadanda suke ba bisa ka’ida ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa Liquified Petroleum Gas LPG wanda kuma akafi sani da gas din da ake dafa abinci da sauran kayan bukatu na rayuwa da gidajen mai da suka ziyarta suna cikin wuraren Karimo, Gwagwa, da kauyen Games kuje da Gwagwalada.
Rahotonni sun bayyana cewa ma’aikatan LPG suna aiki ba bisa ka’ida ba, yayin da aka rufe gidajen mai guda biyu wadanda ake yin aikin su ba tare da lasisi ba.
Mai kula da ayyukan shiyya na Abuja, DPR Uwargida Wilkie Roselyn, ta ce kokarin da ake yi na ganin masu aikin ba bisa ka’ida ba su daidaita harkokin kasuwancin su sun kasa haifar da sakamako mai kyau.
“A yayin gudanar da atisaye na yau, an kai farmaki kan wasu tsirarun LPG guda 11 tare da hadin gwiwar Hukumar Tsaro ta Najeriya NSCDC, An kama wasu ma’aikatan wadannan haramtattun wurare kuma an mika su ga jami’an tsaro don gurfanar da su a gaban kotu.
Wannan ya zama dole mu fita yayin da lamarin ke faruwa, don aiwatar da tanade tanade na dokoki da ka’idojin da suka dace don ginawa da gudanar da ayyukan samar da albarkatun mai, a sashin da ke karkashin ruwa, “in ji ta. Sannan ta yi kira ga duk masu gudanar da ayyukan ba bisa doka ba da su fito su daidaita ayyukan su ta hanyar samun lasisin da ake buƙata don yin aiki daga DPR.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa tawagar ta ziyarci tashoshin mai guda bakwai kuma ta rufe famfunan mai 18 don yin kaifi.