Kungiyoyin fararen hula da matasa a Mali, karkashin jagorancin kungiyar Yerewolo, sun nuna goyon bayansu ga shirin da aka ce Mali na yi na hayar sojojin haya daga Rasha don dakile matsalolin tsaro da suka addabi kasar, kamar yadda Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta yi.
Kakakin kungiyar na Yerewolo, Adama Ben Diarra, ya shaida wa manema labarai cewa idan har kamfanin Wagner, mai sojojin haya zai ceto Syria, da Jamhuriya Afrika ta Tsakiya kamar yadda ake gani a halin yanzu, to ana maraba da shi a Bamako.
A wannan mako da muke ciki ne wasu majiyoyi a Faransa suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Mali na daf da kulla yarjejeniyar dauko sojojin haya har dubu 1000 daga kamfanin Wagner na kasar Rasha.
Wani kakakin ma’aikatar tsaron Mali bai musanta wannan batu na daukar sojojin haya ba, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya fara ruwaitowa a farkon wannan mako.
Sai dai Rasha ta musanta wata tattaunawa da Mali a kan tsaro, bayan da Faransa da Jamus suka yi kashedi a game da hakan.
A watan Mayu, masu zanga zanga suka fito don nuna goyon baya ga jagoran juyin mulkin Mali, Kanar Assimi Goita, inda har suke daga tutar Rasha.
Al’umma Mali da dama na ganin cewa babu abin da Faransa ta tsinana a kasar tun bayan jigbe dakarunta a kasar a shekarar 2013.