Yan bindiga dadi sun kashe Abubakar Abdullahi Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Kasa, reshen Karamar Hukumar Lere ta Jahar Kaduna.
Lamarin Kai harin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, kamar yadda Daraktan Yada Labaru na Kungiyar reshen Jahar Ibrahim Bayero-Zango ya tabbatar wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya, duk da har yanzu babu wani jawabi daya tabbatar da hakan daga Jahar ko Yansanda.
A cewar Mai Magana da yawun Kungiyar, wadanda suka kai harin sun yiwa gidan Shugaban Kungiyar ‘kawanya, da aka fi sani da Dambardi dake garin Lere, da Misalin Karfe 1:00 na dare, kamar yadda Jaridar The Punch
KARANTA WANNAN: Tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa ya koma Jam’iyar APC
Ya Kara dacewa, Yan ta’addan sun bukaci ya basu naira miliyan 20, kafin daga bisani su dauke shi domin hallaka shi akan hanyar Saminaka-Mariri-Zango.
Yace “da Safiyar nan, mutanen mu suka kira Shugaban cin Kungiyar mu na Jaha, tare da sanar da cewa, da misalin karfe 1:00 na daren ranar Juma’a, Yan ta’addan da ba’a san kosu wane ne ba, sun kai hari gidan Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Kasa reshen Karamar Hukumar Lere tare da kashe shi.
“A lokacin da suka iso gidan da Misalin Karfe 1, sun bukaci Naira Miliyan 20 domin ya kwaci kansa, amma ya gaya masu cewa, bai da kudin.
“Duk da ya basu Naira Dubu 250,000, amma sun dauke shi sun kaishi kan hanyar Saminaka-Mariri-Zango inda suka harbe shi har lahira.”
Mai Magana da yawun Kungiyar a lokacin da yake yin Allah wadai da kai harin, ya bukaci Gwamnatin Jahar da Jami’an tsaro dasu yi bincike akan kai harin, tare da gano wadanda suka aikata lamarin.
A wani labarin Kuma
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Cif Luka Barau Dameshi, ya yi murabus na zama memba a jam’iyyar adawa ta PDP, inda Kuma ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Idan za’a iya tuna wa dai, Dameshi ya bar APC Mai Mulki tun a shekarar 2014 zuwa PDP, inda Kuma a yanzu ya bayyana matsayar sa, a cikin wata wasika mai kwanan wata 13 ga Satumba, 202, kuma ya aika zuwa ga shugaban jam’iyyar a mazabarsa dake karamar hukumar ta Ningo/Boher, na karamar hukumar Akwanga a jihar.
Sai dai jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ko da ta nemi sanin dalilin ficewarsa daga PDP zuwa APC a yanzu, ya amsa mata ta sakon kartakkwana cewa, “Tabbas na sauya sheka, kuma shawara ce ta kashin kai.”
Dameshi ya zama mataimakin gwamna a lokacin mulkin farko na Gwamna Umaru Tanko Al-Makura, daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.
Comments 1