By Ishaq Dabai
Akalla dalibai bakwai ne aka ruwaito sun jikkata lokacin da daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Filato a ranar Litinin suka gudanar da zanga zanga kan dage jarabawar su ta semester.
Mahukuntan makarantar sun dage jarabawar saboda wani yajin aikin da malaman makarantar suka fara.
Daliban da ke shirin rubuta jarabawar, sun gamu da kofar makarantar gaba daya a rufe, inda daliban suka fusata suka kuma fito kan tituna don yin zanga zanga amma rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan daba ne suka yi awon gaba da gilashin motoci.
Masu zanga zangar sun toshe hanyar Yakubu Gowon, babban titin da ke shiga da fita daga Jos tare da haddasa cunkoson ababen hawa cikin sa’o’i da yawa.
Da yake magana da manema labarai daya daga cikin daliban, Mista Tindak Theophilius, ya ce daliban da suka ji rauni suna karbar magani a wani asibiti a Jos.Ya ce wasu daga cikinsu marasa lafiyar asma ne da ba za su iya jurewa barkonan tsohuwa da aka harba don tarwatsa daliban ba.
Ya bayyana matakin da hukumar ta dauka na dage jarabawar a matsayin wani yunkuri na takaita tafiyarsu ta ilimi “Mun zo makaranta yau da safe don fara jarabawar mu kawai sa muka samu labarin cewa malaman mu na yajin aiki tun ranar Juma’a.
“Mun shafe sama da shekaru uku a cikin semester daya kawai saboda kullen COVID-19 amma galibi saboda yajin aikin da malaman mu suka fara.” Muna ci gaba da biyan kudin masaukin mu, kudin makaranta, da sauran kashe kudi. tsufa kuma lokacin da muka kammala karatu, ba za mu iya samun ayyukan yi ba saboda tsufa, ”in ji John.
Duk kokarin da mukayi najin ta bakin Mista John Ramadan na sashen hulda da jama’a na cibiyar a lokacin hada wannan labari ya ci tura.